Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito cewa, Hujjatul Islam Sayyid Hashim al-Haidari ya bayyana hakan ne a wani taron gabatarwa kafin babban taron nazarin tunani da gwagwarmayar Shahid Sayyid Hassan Nasrullah, wanda aka gudanar a ƙarƙashin taken “Shahid Sayyid Hassan Nasrullah: Jagora a Tafarkin Tsayin Daka da Yaƙi da Zalunci”, a birnin Qum na ƙasar Iran.
Sayyid Hashim Al-Haidari ya ce ɗaya daga cikin fitattun siffofin Shahid Nasrullah ita ce tsananin ƙaunarsa da goyon bayansa ga Wilayatul Faƙih da jagoran wannan tsarin a zamaninsa. Ya bayyana cewa Nasrullah ya shafe fiye da shekaru goma sha biyar yana jaddada muhimmancin kare wannan aƙida a fili, yana mai cewa bai kamata mutum ya daina kare ta ba, ko da kuwa hakan zai jefa rayuwarsa cikin haɗari.
Ya ƙara da cewa Shahid Nasrullah yana ganin Wilayatul Faƙih a matsayin wani ginshiƙi na aƙida da addini, wanda yake da alaƙa da tushen tunanin Musulunci. Saboda haka, yana ganin wajibi ne a yi wa al'umma bayani a kansa cikin harshe mai sauƙi da fahimta.
Wilayatul Faƙih da Tushen Halaccin Gwagwarmaya
Hujjatul Islam Sayyid Hashim Al-Haidari ya bayyana cewa, a fahimtar Shahid Nasrullah, halaccin gwagwarmaya ma yana da tushe ne a Wilayatul Faƙih. Don haka, kare wannan aƙida wani ɓangare ne na nauyin addini da aƙida, ba batun siyasa kawai ba.
Ya ce Nasrullah yana ganin cewa domin a fahimci tafarkin gwagwarmaya yadda ya kamata, dole ne a fahimci tushen aƙida da addinin da ya ginu a kansa. Saboda haka, ya ɗauki kare Wilayatul Faƙih da bayyana tushen addinin gwagwarmaya a matsayin muhimman ginshiƙai na tunaninsa da ayyukansa.
Biyayyar Shahid Nasrullah ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Sayyid Al-Haidari ya kuma yi bayani kan irin zurfin imani da biyayyar da Shahid Nasrullah yake nunawa ga Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, tsohon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran. Ya ce Nasrullah yana da cikakkiyar biyayya gare shi, har ma idan ya yi zaton cewa jagoran yana da wani buri ko fata, zai yi ƙoƙarin aiwatar da shi.
Ya bayyana cewa Nasrullah yana kallon jagoran ne a matsayin wakilin Imam Mahdi (AF), bisa fahimtarsa ta addini, ba wai saboda alaƙar siyasa ko mu'amalar yau da kullum kawai ba.
Sayyid Hashim Al-Haidari ya nakalto Nasrallah yana cewa: “A kullum, ina yin addu'a sau da dama cewa Allah Ya ɗauki sauran rayuwata Ya ba Jagora.”
Ya ƙara da cewa ƙauna da girmamawar Nasrullah ga jagoran sun kai matsayin da wasu mutane suke ganin halartar taron Nasrullah tamkar halartar taron jagoran ne, saboda yadda yake nuna biyayya ga jagorancin da ya yi imani da shi.
Muhimmancin Ayyukan Al'adu da Tarbiyyar Addini
Hujjatul Islam Sayyid Hashim Al-Haidari ya ce Shahid Nasrullah yana ba ayyukan al'adu muhimmanci sosai, domin yana ganin al'adu su ne tushen gina sauran ayyuka. Ya bayyana cewa Nasrullah bai yarda a dakatar da ayyukan al'adu saboda rikice-rikice ko yanayin tsaro ba, sai dai ya kamata a ci gaba da su ko da a lokacin yaƙe-yaƙe da matsaloli.
A cewarsa, Nasrullah yana ganin cewa dole ne a raya imani, aƙidar Wilayatul Faƙih da tunawa da lahira a tsakanin tsararraki. Ya ɗauki ci gaba da ayyukan al'adu a matsayin ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin cimma wannan buri.
Hujjatul Islam Al-Haidari ya kuma bayyana cewa wannan tunani na Nasrullah ya taimaka wajen ƙarfafa aƙida da imanin mambobin ƙungiyar Hizbullah, musamman ta fuskar fahimtar addini, Wilayatul Faƙih da muhimmancin tarbiyyar al'adu.
Jaddada Aminci ga Imam Khamenei a Daren Ashura
Hujjatul Islam Sayyid Hashim Al-Haidari ya bayyana cewa Shahid Nasrullah ya kasance yana jaddada amincinsa ga Imam Khamenei a duk lokacin bukukuwan Ashura da ake gudanarwa a birnin Beirut na ƙasar Lebanon.
Ya ce a duk shekara, dubban ɗaruruwan mutane kan taru a Beirut a daren Ashura da ranar Ashura, inda Nasrallah yake jaddada alƙawarin da ya ɗauka na kasancewa tare da jagoran.
A cewarsa, Nasrallah yana amfani da kalaman sahabban Imam Husaini (AS) a daren Ashura wajen bayyana amincinsa. Sahabban Imam Husaini (AS) sun bayyana cewa ko da za a kashe su sau dubu, sannan a sake rayar da su, ba za su taɓa barin Imam ɗinsu shi kaɗai ba.
Al-Haidari ya ce Nasrullah ya kasance yana maimaita wannan furuci a Beirut, a gaban dimbin jama'a:
«مَا تَرَكْنَاكَ يَا ابْنَ الْحُسَيْنِ، أَيُّهَا الْإِمَامُ الْخَامِنَئِي»
Ma'ana: “Ya kai ɗan Husaini, ya Imam Khamenei, ba za mu taɓa barin ka kai kaɗai ba.”
Ya bayyana cewa wannan furuci yana nuna yadda Nasrullah yake danganta amincinsa ga jagoran da aƙidarsa ta Wilayatul Faƙih.
Jawabin Nasrallah Kan Nasarorin Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Hujjatul Islam Sayyid Hashim Al-Haidari ya kuma tuna da wani jawabin da Shahid Nasrullah ya gabatar a shekarar 1397 bayan hijira ta rana(2018), a daidai lokacin bikin cika shekaru arba'in da nasarar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran.
Ya ce a makonnin da suka gabaci ranar 22 ga watan Bahman na wannan shekara, ya ziyarci Nasrullah a Beirut. A lokacin ganawarsu, Nasrullah ya sanar da shi cewa yana shirin gabatar da jawabi kan ci gaba da nasarorin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu a ƙarƙashin jagorancin Wilayatul Faƙih.
A cewar al-Haidari, Nasrullah ya shafe kusan awa ɗaya da rabi yana magana kan ci gaba da nasarorin Iran a fannoni daban-daban.
Kare Iran Duk da Matsin Lamba
Sayyida Hashim Al-Haidari ya bayyana cewa goyon bayan da Nasrullah yake bai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya samo asali ne daga imaninsa da ƙarfin halinsa. Ya ce Nasrullah bai kasance yana ɗaukar irin waɗannan matsayoyi saboda tilas ba, domin ya fuskanci matsin lamba mai yawa, amma duk da haka ya ci gaba da bayyana ra'ayinsa a fili.
Ya ƙara da cewa Nasrullah ya kasance yana magana kan nasarorin Iran duk da matsin lamba da takunkuman da ƙasar take fuskanta. A cewarsa, Iran ta samu nasarori da dama duk da ƙalubalen da take fuskanta, kuma tana da muhimman damar ci gaba ta fuskar ruhi da addini.
Hujjatul Islam Al-Haidari ya yi kira ga al'ummar Iran da su ƙara lura da nasarorin da ƙasarsu ta samu, tare da ba da muhimmanci ga tsarin Jamhuriyar Musulunci da jagorancinta.
A ƙarshe, ya jaddada cewa kalaman Shahid Sayyid Hassan Nasrullah da matsayoyinsa sun nuna irin muhimmancin da yake bai wa Wilayatul Faƙih, kare tushen gwagwarmaya, da kuma ci gaba da ayyukan al'adu da tarbiyyar aƙida. Ya kuma yi kira ga al'ummar Iran da su ƙara fahimtar nasarorin ƙasarsu da kuma muhimmancin rawar da jagoranci yake takawa a tsarin Jamhuriyar Musulunci.
Ra'ayinka